Muhimmancin Karadua Ga ‘Yan Yankin

Posted by Buhbat in Sep 06, 2010, under Uncategorized

Ranar Litinin za mu yi hira da Habib Rabiu Dandutse akan “Muhimmancin Karadua Ga ‘Yan Yankin.” Sai ku biyo mu domin jin yadda mukayi da shi.

Comments Off more...

Habibullah Abin Koyi ne!

Posted by Buhbat in Sep 03, 2010, under Uncategorized

Ganin irin yadda harkokin siyasa su ka zama abinda suka zama a kasa mai tasowa kamar Najeriya, ba karamin kalubale bane matasa zasuyi a kokarin ganin cewa suma an dama da su a cikin harkokin siyasa. Musamman ganin cewar yadda ‘yan siyasar kasar ke yin amfani da wasu da yawa daga cikin su matasan wajen yin magudi da kawo rigingimu da kuma tashe-tashen hankuli a sa’ilin da su ke neman kujeru. ‘Yan siyarsar kasar dai su kan yi hakan ne ta hanyar jahiltar da su matasan, da kuma basu miyagun kwayoyi da zasu fitar da su daga cikin hankulansu, da makamai da kuma basu goyon baya domin tada rikice-rikice na ba gaira babu dalili.

Ga matasa wandanda suka rigaya suka afka cikin wannan irin mummunan tarkon azzaluman ‘yan siyasa yana da matukar wahala sosai su gane cewa ana amfani ne dasu kawai, bayan kuma an samu biyan bukata sai a yardasu. An ci moriyar ganga. Akan kuma nemesu har ila yau idan wata bukatar amfanin nasu wajen yin wani mummunan aikin ya taso.

Duk da irin wadannan koma baya da rashin fuskantar siyasa ta ainufi, Habibullah ya yi kokarin bincike da ganewa tare da fitar da kansa daga aikata hakan. Ba wai kuma ya tsaya a nan bane kawai, sai da ya yi kokarin janyo hankulan matasa ‘yan uwanshi, ya kuma nuna masu zahirin abubuwan da ke faruwa.

Ni shaidane akan hakan, domin kuwa gab da zaben da ya gabata na kansiloli na shekara 2007 na samu muhimmiyar damar ganawa da shi. Ga kuma yadda hirarmu ta kaya;

Buhari:

Hon. Habibullah nayi matukar farin cikin samun damar hira da kai sosai domin ina da tambayoyi da dama da na dade ina neman amsoshinsu daga gareka.

Habib:

Mallam Buhari Fidbaks, idan ma ka kira ni Habib ya wadatar. Kuma nima na ji dadi matuka yadda ka nuna cewa kana neman fahimtar wannan manufa da muke yadawa. Sannan ina fatan samun damar amsa tambayoyinka Insha’Allah.

Buhari:

To amin. Kafin mu yi nisa ina son in sani a takaice waye Habib?

Habib:

To nidai sunana na yanka Habibullah. An haifeni a 24 ga watan Maris shekara ta 1989 a nan cikin garin Funtua. Na yi makarantar primary ta Ideal Int’l School na shekaru shida, daga inda na ci gaba zuwa secondary a Ulul-Albab Science Secondary School dake garin katsina, inda daga bisani kuma na yi transfer zuwa Govt. Science Secondary School da ke karamar hukumar Kankara a in da na kammala karatun na gaba da secondary.

Buhari:

Menene mafarin shiga cikin harkar siyasa da kayi da zurfi haka kuma da yarintarka ?

Habib:

Mafarin shigata cikin harkar siyasa na kuma zurfafa kamar yadda kace dai ya samo asali ne daga nazurran da na yi da jimawa kan irin yadda harkokin siyasa ke tafiya tun lokacin mutuwar Gen. Sani abacha a shekara ta 1999. Duk da cewa a wadancan lokuttan shekaruna ko kuma wasu zasu iya cewa tunani irin na karamin yaro kama ta a wannan lokacin bai isa matakin maida hankali dangane da hakan ba. To amma ni gaskiya ko a wannan lokaci na dade da gane cewa wasu daga cikin ‘yan siyasar nan kawai suna amfani da matasa ne  domin cika burinsu ba wai da niyar taimakonsu domin gyara rayukan su matasan ba. Ni kuma ganin hakan yasa na sha alwashin kin fadawa cikin irin wannan yanayi wanda zai bada damar ayi amfani da kuruciya da yarintata domin cimma wata manufa wadda ba za ta amfani kasa, ko al’umma ko ci gaban siyasa ba. Wannan shine sanadin dayasa na tashi nayi kira ga matasa domin jawo hankulansu. Kuma zan iya cewa na samu gaggarumar nasara wajen yin hakan.

Buhari:

Na san cewa duk da samun nasarar da kayi, akwai wasu matsaloli da ka fuskanta. Kamar wadanne irin matsaloline?

Habib:

Dama idan yau ka tashi da niyar zuwa Kano ai kasan akwai tafiya. Gaskiya na fuskanci kalubale musamman daga wajen matasa na gaba dani a shekaru. Kasan Nigerian Factor. Su suna ganin cewa ya za’a yi yaro kamar wannan haka ya kawo mana wasu abubuwa haka da dai sauransu. Ni kuma sai nayi kokarin nuna masu cewa ba wai shekaru ake magana ba, a’a ina kokarin bude masu dayan idonsu  da mugayen ‘yan siyasa suka kulle da basu kudi da kwayoyi da sauransu. Amma kuma daga baya an samu nasara wasu daga cikinsu sun fahimci hakan. Dayar matsalar da ita ma rage ma kekenmu gudu itace shawarar da mukayi ta cewa ba za muyi campaign da kudi ba. To gaskiya ya dauke mu lokacin da ba mu yi tsammani ba kafin shawo kan matasan. Maimaikon yin amfani da kudi, sai muka yi amfani da ilmantar da matasa a kan cewa siyasar kudi siyasa ce ta saida ‘yanci a maimakon kwato shi. Bayan dai duka wahalhalun da muka sha Alhamdulillah mun samu nasarar wayar da kan da dama daga cikin matasan. Kuma sun fuskanci manufarmu sun kuma bamu hadin kai.

Buhari:

Menene ya baka karfin gwiwar jurewa har ka kai inda ka ke a yau?

Habib:

Anan ina iya cewa abinda bature ke kira Hope, wato ma’ana amanna da cewa akwai yiwuwar samun nasara a gaba, shi ya bani karfin juriya. Sannan kuma irin yadda naga su kansu ‘yan uwana matasa maza da mata sun bada hadadden goyon baya da hadin kai da yadda suka nuna kishi da son samun canji da cigaba, hakan ma ya karfafa min gwiwa matuka.

Buhari:

Ganin irin nasarar da ka samu da kuma matsalolin da ka samu, yasa nake son tambayar ka cewa akwai yiwuwar cewa zaka ci gaba da yada wannan manufa taka ko kuwa?

Habib:

Yada manufa kam yanzu muka fara. Wato shi irin wannan aiki mafari gareshi ba shi da karshe. Dalilin da yasa na ce haka kuwa shine,  shi a kullum shi azzalumi neman hanyar yin zalumci yake yi a ko da yaushe, to ke nan don ka kori akuya bakin hatsi, to kana shigewa zata dawo. Saboda haka, mu mune masu hatsi, kuma zamu ga yadda akuya zata ci hatsinmu.

Buhari:

Daga karshe wane irin kira da kuma shawara za ka ba matasa?

Habib:

Kiran da zanyi ga matasa da babbar murya shine su nemi su san shi menene siyasa. Sannan su sani cewa ‘yancinsu yafi mutunci da daraja akan kudin da ake amfani dasu wajen jawo hankullansu. Sannan har ila yau shawarar da zan ba matasa ita ce hanyar fuskantar ingantacciyar siyasa, ba siyasar banga ba, guda daya ce: ita ce  ta hanyar shiga cikin ta! Ta hakan ne kawai zaka iya tace ta, ka fidda gari sannan ka kuma fidda tsaki daga cikinta. Saboda haka ina shawartar matasa da su sa hannu dumu-dumu cikin harkokin siyasa a kowane mataki. Ta haka ne za’a samu irin canji da cigaban da muke nema. Wato su fa matasa sune kashin bayan kowace al’umma. Sune ke sa tayi kyau idan suka shiga. Rashin shigarsu kuma shi ke ba miyagu daman yin batanci. Saboda haka ya kamata mun sani.

41 Comments , , , , , more...

Tools ‹ Shafin Dandali Blog

Posted by Buhbat in Sep 03, 2010, under Uncategorized

Comments Off more...

Shafin Farko

Posted by Buhbat in Sep 03, 2010, under Uncategorized

Barka Da  Zuwa Dandali.blog.com.

Wannan dandali dandaline mai zaman kanshi wanda ke yada manufar Hon. Habibullah Rabiu Dandutse, wanda aka fi sani da Habib a takaice, na cewa matasa musamman na jihohin da ke yankin Arewacin Najeriya da su shiga cikin harkokin siyasa a matakai daban-daban na Najeriya kama daga na unguwa, na karamar hukuma, na jiha da ma mataki na tarayya baki daya.

Ita dai wannan manufa mun fara yadata ne a shekara ta 2007 bayan kwarin gwiwa, hazaka, kwazo da kuma kishin matasan kasa da shi Habib din ya nuna ta hanyar fitowa takarar kansila a mazabarsa ta Unguwar Musa Ward da ke yankin karamar hukumar Funtua a jihar Katsina . Bayan ganin irin rawar da ya taka, duk da kuwa cewa bai samu nasarar kai labari a babban zabe ba, wannan shine musabbabbin da ya sa mu kuma sauran matasa muka yaba da kokarinsa sannan kuma muka fito domin nuna masa goyon baya.

Nan ba da jimawa ba wannan dandalin zai kakkafa rassa a ko ina cikin fadin kasarnan zuwa kowace jiha ckin jihohi 36 na Najeriya. Hakan shine zai ba matasa daman fitowa da ra’ayoyinsu da muryoyinsu da kuma sanin hakkokinsu da muhimmancinsu da irin rawa da kuma gudummuwar da za su iya bayarwa ga ci gaba ta fannin siyasa a Najeriya.

Comments Off more...